in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani ma'aikacin lafiya na Guinee da ya warke daga Ebola ya yi kira da kada a nuna shakku kan cutar
2014-08-30 15:57:29 cri
Bakary Oulare, wani ma'aikacin lafiya na kasar Guinee da ya warke daga cutar Ebola, a cikin wani bahasinsa da wasu kafofin watsa labarai na gwamnatin kasar suka rawaito a ranar Jumma'a, sun ce ya yi kira ga 'yan kasar na Guinee da kada su nuna shakku game da bullowar cutar Ebola a kasar Guinee da yin kira ga hada kai wajen yaki da cutar.

Sakon da ya aika wa 'yan kasa, shi ne ya gaya wa masu maganar gaskiya, cewa zazzabin Ebola akwai shi a kasar Guinee. Ba harkar siyasa ba ce, kuma ba wata hanya ba ce ga hukumomin kasar wajen neman kudi, kamar yadda wasu suke zato a kasar ta hanyar jita jita, in ji mista Oulare, ma'aikacin likatar dake aiki a cibiyar yaki da cututtukan dake yaduwa ta Donka, muhimmiyar cibiyar asibiti ta jami'a ta kasar Guinee. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China