in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cutar Ebola ta kashe wani likita a birnin Patakwal dake kudancin Najeriya
2014-08-28 19:12:28 cri

Yau ranar Alhamis, ministan kiwon lafiya na tarayyar Najeriya Dr. Onyebuchi Chukwu ya tabbatarwa manema labarai a Abuja cewa, cutar nan mai kisa wato Ebola ta kashe wani likita a birnin Patakwal mai arzikin man fetur a kudancin Najeriya, lamarin da ya sa zuwa yanzu mutane shida suka rasa rayukansu sakamakon Ebola a Najeriyar.

Ministan ya ce, wannan likita ya mutu ne a ranar 22 ga wata, wanda shi ne daya daga cikin wadanda suka yi wa wani jami'in ECOWAS jinya bayan da yi mu'amala da dan kasar Laberiya wanda ya shigo da cutar Ebola cikin kasar Najeriya, wato marigayi Patrick Sawyer. Jami'in ECOWAS wanda aka yi masa jinya ya warke daga cutar, amma wannan likita daga birnin Patakwal ya kamu da cutar har ma ya mutu.

Wannan shi ne karo na farko da aka samu wanda ya mutu sakamakon cutar Ebola a wata jihar da ba ta Lagos ba a Najeriya.

Tuni an ce Najeriya ta samu gagarumar nasara wajen dakile cutar Ebola mai yaduwa. Wani babban jami'in da sakatare-janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya nada kan harkar daidaita cutar Ebola wato Dr. David Nabarro ya kawo ziyara birnin Abuja jiya ranar Laraba, inda ya jinjinama kokarin da gwamnatin Najeriya ke yi a fannin jan birki ga yaduwar cutar, haka kuma shugaban kasar Goodluck Jonathan ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da nuna jajircewa domin murkushe wannan cuta a Najeriya.

A hannu guda kuma, ministan kiwon lafiyar Najeriya Dr. Onyebuchi Chukwu ya ja kunnen 'yan kasar yana mai gargadi cewa, kar a yi sakaci kan cutar Ebola, saboda har yanzu ba'a kawar da ita baki daya daga kasar ba. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China