in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta fitar da jadawalin shawo kan Ebola a yammacin Afrika
2014-08-29 10:09:28 cri

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO a ranar Alhamis din nan ta fitar da wani sabon jadawali da zai yi jagora da shirya martani yadda kasashen duniya za su dauki matakai a kan cutar Ebola da ya ratsa a yammacin Afrika.

Hukumar ta WHO ta ce, makasudin wannan jadawali shi ne samar da dabarun hana yaduwar cutar a sauran kasashen duniya nan da watanni 6 zuwa 9, sannan kuma a yi saurin lura sakamakon da yaduwar cutar da za ta haifar.

Wannan jadawali ya zo ne sakamakon bukatar gaggawa da ya bukaci sauran kasashen duniya su zage damtse na samar da kariya, musamman yadda kashi 40 na cikin 100 na yaduwar cutar ya auku a cikin makonni 3 da suka gabata.

Har ila yau jadawali zai zama kamar wata hanya ta kara samar da bayanai a kai a kai game da tsarin da ake bi dalla dalla. Ana mai da hankali matuka a kan cibiyoyin jinyar masu dauke da cutar da kiyaye yaduwar ta, kafofin wayar da kan jama'a da hanyar rigakafin lokacin jana'izar wadanda suka mutu sakamakon cutar.

A kasashe dake da bayanai na yaduwar cutar da yadda ake saurin kamuwa da ita, wannan jadawalin ana sa ran zai canza hanyar da ake bi a baya wajen tunkarar sabbin wadanda suka kamu da cutar cikin watanni 3, hana yaduwar cutar a manyan biranen kasashe, manyan tashoshin jiragen ruwan kasashe, da duk sauran hanyoyin da suka shafi na mahalli a cikin watanni 6 zuwa 9.

A kasashe da bayanai ya nuna yaduwar cutar dalilin cudanya da masu dauke da cutar, wannan jadawalin zai taimaka wajen aiwatar da matakai na gaggawa, da kuma tabbataccen tsarin, sannan kuma a hana yaduwar cutar cikin makonni 8. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China