Hukumar lafiya ta WHO ta tabbatar da janyewar ma'aikatan kula da lafiyarta daga yankin Kailahun na kasar Saliyo, yankin da ke kan gaba wajen yawaitar yaduwar cutar Ebola a kasar.
WHO ta ce, ma'aikatan sun janye daga yankin ne na dan lokaci, ya zuwa Freetown, babban birnin kasar, bayan daya daga ma'aikatan lafiyar ya harbu da cutar.
Wata sanarwa da WHOn ta fitar ta rawaito wakilinta a kasar Saliyo Daniel Kertesz, na cewa, daukar wannan mataki ya dace kwarai, duba da yadda ma'aikatan ke cikin wani irin hali na damuwa sakamakon kamuwa da dayan su ya yi da cutar.
Wannan ma'aikaci dai shi ne na farko da ya kamu da cutar ta Ebola, karkashin inuwar ma'aikatan hukumar ta WHO. Ko da yake WHOn ta ce, da zarar an kammala bincike tare da daukar matakan da suka kamata, za a sake mayar da tawagar bakin aiki a yankin na Kailahun. (Saminu)