Hukumomin Amurka sun sanar a ranar Alhamis cewa za'a fara kaddamar da gwaje-gwajen farko na wata alluar gwaji a kan dan adam a mako mai zuwa bisa kokarin yaki da cutar Ebola, wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 1500 a yankin yammacin Afrika.
Hukumomin kiwon lafiya na Amurka (NIH) sun bayyana a cikin wata sanarwa cewa, matakin farko na gwajin a asibiti zai taimaka wajen fayyace idan allurar da aka kirkiro cikin hadin gwiwa tsakanin hukumar kasa kan cututtuka masu yaduwa (NIAID) dake daya daga cikin hukumomin kiwon lafiya na NIH, da kuma cibiyar binciken magunguna na GlaxoSmithKline (GSK) na da inganci da bullo da wata kariyar jiki mai kyau daga wannan cuta.
A cikin tsarin wannan gwaji, da zai gudana a wani asibitin NIH dake Bethesda na jihar Maryland, wasu baligai masu koshin lafiya 20, masu shekarun haifuwa daga 18 zuwa 50, za'a yi masu allurar ta hanyar jijiya, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)