Ban Ki-moon dake ziyarar aiki yanzu haka a kasar Faransa, zai tashi daga birnin Paris zuwa kasar Afrika ta Kudu, domin ya halarci bikin karrama mista Mandela da za'a shirya a ranar Talata in ji kakakin MDD tare da jaddada cewa mista Ban zai koma New York a ranar Laraba mai zuwa.
Allah ya wa Nelson Mandela cikawa a ranar Alhamis a birnin Johannesburg a yayin da ya ke da shekaru 95 a duniya.
A ranar Jumma'a, MDD ta nuna bacin ranta game da mutuwar Mandela, jarumin kare zaman lafiya wanda ya jagoranci yaki da wariyar launin fata, tare da karrama babban tarihin da wannan babban mutum ya bar wa duniya.
Tutocin MDD dake gaban cibiyar MDD dake birnin New York an sauko da su kasa. Haka kuma manyan kungiyoyin MDD biyu, babban taron MDD dake kunshe da mambobi 193 da kuma kwamitin tsaro na MDD dake kunshe da mambobi 15 kowane daga cikinsu sun kebe lokaci nuna alhini da girmama ga Mandela, mutumin da ya kwashe shekaru 27 gidan yari kafin ya zama shugaban kasar Afrika ta Kudu na farko bakar fata.
Ranakun zaman makokin kasa na Mandela, wanda ya samu kyautar Nobel ta zaman lafiya a shekarar 1993 za'a gudanar dasu a ranar 15 ga watan Disamba. (Maman Ada)