Mr. Ban wanda ya gabatar ma babban taron MDD rahoton karshe da tawaga mai bincike kan batun yin amfani da makamai masu guba a kasar ta Syria ta tattara, ya kuma bayyana cewa, shaidu da bayanan da tawagar binciken ta samu, sun tabbatar da cewa an taba yin amfani da makamai masu guba kan sojoji, da fararen hulan kasar a wurare daban daban, lamarin da ya sanya shi damuwa matuka.
Mista Ban ya ce ya yi matukar Allah wadai da matakin amfani da makamai masu guba, wanda babban laifi ne da ya sabawa halayyar martaba rayuwar dan Adam.
A sa'i daya kuma, mista Ban ya yi maraba da ci gaban aikin lalata makamai masu guba a kasar Syria da aka yi a 'yan watannin nan, yace hakan ci gaba ne da aka samu bisa kokarin gamayyar kasa da kasa.
A dai wannan rana, ita ma babbar jami'ar MDD mai kula da aikin kwance damarar soja Angela Kane, da shugaban tawagar binciken makamai masu guba a kasar Syria Ake Sellstrom, sun kira wani taron manema labaru a hedkwatar MDDr, inda suka bayyana yanayin da ake ciki wajen gudanar da binciken, gami da jaddada cewa, binciken bai shafi tantance wane bangare ne ya fara kai farmaki da makamai masu gubar ba, don haka sakamakon da aka samu shi ma ba zai fayyace hakanba. (Bello Wang)