Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, ya gana da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a birinin Shanghai na nan kasar Sin.
Jagororin biyu dai sun gana da juna ne a ranar Talata, yayin da suke halartar taron koli na hudu, na tattaunawa kan inganta cudanya da karfafa hadin gwiwa a nahiyar Asiya na CICA da ake yi a birnin na Shanghai.
Rahotanni dai sun ce Mr. Ban da shugaba Putin sun yi musanyar ra'ayoyi, kan muhimman lamuran da suka shafi duniya da na shiyya-shiyya. Inda kan batun rikicin siyasar Ukraine, suka bayyana aniyarsu ta daukar matakan warware batun a siyasance, tare da goyon bayan tattaunawa ta fuskar siyasa wadda ka iya kawo karshen lamarin cikin ruwan sanyi.
A kan batun Sham kuwa, Babban magatakardar MDD da shugaba Putin sun nazarci hanyar da ta dace a bi wajen warware batun, tare kuma da batun hanyar ba da tallafin jin kai ga al'ummar kasar.(Kande)