A wannan rana, a gun taron 'yan jarida karo na farko da aka yi a wannan shekarar a New York, cibiyar MDD, Ban Ki-moon ya ce, a yayin da ake mai da hankali kan samun ci gaba da zaman lafiya, ana fuskantar matsalar rikici dake kara tsananta a yau da kullum a duniya, kamar yadda ake a Syria, Sudan ta Kudu, Afirka ta Tsakiya da sauransu, hakan ya yi babbar illa ga rayuwar fararen hula na wadannan kasashe.
Ban da haka, Ban Ki-moon ya kara da cewa, a bana kamata ya yi kasashen duniya su kara mai da hankali da nuna goyon baya ga matsalolin da ake fuskanta a yanzu, tare da ci gaba da taimakawa Afghanistan da sauransu dake cikin yanayin rikon kwarya. Kuma yana sanya ran cewa, za a samu babban ci gaba a fannin daidaita rikici tsakanin Palestinu da Isra'ila.
Dadin dadawa, Ban Ki-moon ya kara da cewa, bana shekara ce mai muhimmanci kwarai wajen cimma muradun karni na MDGs kafin zuwan wa'adin karshe da aka tsara a badi. Kamata ya yi inji shi a samu babban ci gaba wajen tsara shirin samun bunkasuwa bayan shekarar 2015 yadda ya kamata.(Fatima)