in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Sudan
2014-08-20 11:04:50 cri
Sojojin kasar Sin masu aikin kiyaye zaman lafiya dake kunshe da hafsoshi da sojoji 105 sun tashi daga birnin Jinan na lardin Shandong da ke gabashin kasar zuwa yankin Darfur na kasar Sudan a daren 19 ga wata.

Sojojin dai za su kula da aikin gina filayen jiragen sama da gadoji, da gyara hanyoyin mota da dai sauransu.

Tun bayan da aka kafa wannan rundunar soja a watan Yuni na bana, sojojin sun samu horo a fannonin yin amfani da na'urorin gine-gine, tuka mota a kan hanyoyi marasa kyau, bada jinya da dai sauransu. Kana sun koyi ka'idojin kiyaye zaman lafiya na MDD, ladabi, harshen Turanci, al'adun da tsarin addinin mazauna yankin da za su gudanar da aikinsu. Ban da wannan kuma, an samar wa sojojin magunguna da na'urori na musamman don magance kamuwa da cutar Ebola da kuma bada jinya ga mazauna wurin da suka kamu da cutar.

A ranar 27 ga watan Agusta ne ake sa ran kara tura hafsoshi da sojoji 120 masu kiyaye zaman lafiya zuwa kasar ta Sudan. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China