in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Venezuela ya gana da 'yan wasan kasar sa wadanda za su halarci gasar birnin Nanjing
2014-08-15 09:31:58 cri
Shugaba Nicolas Maduro na Venezuela, ya gana da tawagar 'yan wasan kasar sa, wadanda za su halarci gasar Olympic ajin matasa a birnin Nanjing na nan kasar Sin, tun daga ranar 16 zuwa 28 ga watan nan na Agusta.

Shugaba Maduro wanda ya gana da tawagar a Alhamis din da ta gabata a fadar sa ta Miraflores, ya ce tawagar mai kunshe da mutane 59, tana wakiltar daukacin matasan kasar ne baki daya. Ya ce yana fatan mambobin tawagar za su kafa wani tarihi abin koyi, wanda zai kunshi ci gaba, da nuna da'a, tare da mutunta abokan wasa.

A shekaru 4 da suka gabata 'yan wasan kasar ta Venezuelan 21 ne suka halarci makamanciyar wannan gasa a kasar Singapore, suka kuma fafata a wasanni 10.

Yayin ganawar da tawagar ta wannan karo ta yi da shugaba Maduro, mai rike da tutar ta Robeilys Peinado, wanda ya taba lashe lambar Azurfa ta tsallen kwangwala a gasar wasannin masata ta duniya, kana ya lashe lambar Zinari a gasar wasannin kawancen nahiyar Amurka, ya ce tawagar na matukar fatan kare tutar kasar ta hanyar kwazo, da jajircewa, kaunar kasa da kuma maida hankali matuka.

Kaza lika a yayin wannan ganawa shugaba Maduro ya mika wata lambar yabo ta musamman, ga kungiyar kwallon Kwando ta kasar, sakamakon lashe gasar nahiyar Kudancin Amurka karo na 46 da kungiyar ta yi cikin watan Yulin da ya shude. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China