in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manchester City ta yi hayar Lampard
2014-08-07 19:58:21 cri
Manajan kulob din Manchester City Manuel Pellegrini, ya tabbatar da cewa kulob dinsa zai karbo bashin tsohon dan wasan tsakiyar Chelsea Frank Lampard daga New York City FC wanda Lampard din ke takawa leda a yanzu.

New York FC dai daya ne daga cikin kuloblika 2 da ke da kyakkyawar hulda da Manchester City. Kuma a cewar Pellegrini, Lampard zai fara bugawa Manchester City wasa daga ranar Laraba, ya zuwa lokacin da za a kaddamar da sabuwar kakar wasannin MLS a shekara mai zuwa, inda zai koma bugawa kungiyar sa ta New York FC wasanni a watan Janairu mai zuwa.

Komawar Lampard dan shekaru 36 gasar Premier dai na iya ba shi damar kara buga wasannin kasa da kasa. Kamar yadda a baya ya ciwa kulaf din kasar Ingila kwallaye 29 cikin wasanni 106 da ya buga.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China