in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na fatan ba da gudumawa ga bunkasuwar yankin Asiya da Pacific
2014-08-20 16:46:57 cri
Wakilin majalisar gudanarwa ta kasar Sin Yang Jiechi ya ce, kasar Sin ta kasance daya daga iyalan yankin Asiya da Pacific, kana yankin Asiya da Pacific shi ne tushen kasar Sin ta fuskar burinta na neman bunkasuwa.

Hakan a cewar Mr. Yang shi ne dalilin da ya sanya kasar ta Sin fatan ciyar da wannan yanki na Asiya da Pacific gaba, ta hanyar bunkasuwar kanta, da kuma samar da damar ci gaban yankin gaba daya ta hanyar bude kofofinta.

Wakilin majalisar gudanarwar kasar ta Sin wanda ya bayyana hakan yayin bikin bude taron manyan jami'an kungiyar yin hadin gwiwa a yankin Asiya da Pacific ta fuskar tattalin arziki wato APEC karo na uku wanda ya gudana a Larabar nan, ya kara da cewa, tsahon lokaci kasar Sin na da tunani kan yadda za ta iya ba da gudumawa ga ci gaba da dunkulewar tattalin arzikin yankin Asiya da Pacific.

Mr. Yang ya ce a wannan lokaci da take karbar bakuncin taron kungiyar APEC na bana, Sin na da fatan amfani da wannan dama wajen inganta hadin gwiwar kasashen yankin, ta yadda za a iya samar da karin dabarori, da kuma kokartawa wajen samun sakamako mai gamsarwa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China