A daren yau ne kuma, za a bude taron Shangri-La a Singapore. Game da wannan batu, Qin ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, wannan muhimmin dandali ne na yin shawarwari kan harkokin tsaron Asiya, shi ya sa Sin take dora muhimmanci sosai a kai.
An labarta cewa, mataimakin babban hafsan hafsoshin rundunar sojan 'yantar da jama'ar kasar Sin, Wang Guanzhong zai jagoranci tawagar Sin domin halartar taron, yayin da darektar kwamitin harkokin waje na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, madam Fu Ying ita ma za ta halarci taron bisa goron gayyata.(Fatima)