in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron tattaunawa a tsakanin Sin da kasashen da ke yammacin Asiya da arewacin Afirka a birnin Yiwu
2014-05-27 15:19:18 cri

A ranar Talata 27 ga wata, an kira taron tattaunawa a tsakanin Sin da kasashen da ke yammacin Asiya da arewacin Afirka a birnin Yiwu na lardin Zhejiang.

Hukumar kula da cudanya da kasashen waje ta kwamitin tsakiya na JKS da gwamnatin lardin Zhejiang suka karbi bakuncin wannan taro cikin hadin gwiwa bisa taken "kishin zuci don kyakkyawar makoma". A tsawon kwanaki biyu, wakilan cikin gida da na waje za su tattauna kan yadda za a yi kwaskwarima don samun ci gaba, da kuma yadda za a yi hadin kai don neman samun nasara tare.

Ma Biao, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin ya furta a gun bikin kaddamar da taron, cewar inganta hadin gwiwa da cudanya a tsakanin Sin da kasashen da ke yammacin Asiya da arewacin Afirka, ba ma kawai zai karfafa dankon zumunci a tsakaninsu ba, hatta ma zai kara azama ga amincewar juna a siyasance, da cudanyar al'adu, da kuma ba da taimako ga juna a fannonin albarkatu, kudi, da kasuwanci, ta yadda za a amfana wa jama'ar wadannan kasashe. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China