Wata sanarwar da kakakin sa ya fitar, ta ce harin na jiya Asabar ya sabbaba jikkatar karin wasu ma'aikatan tawagar ta MINUSMA su 7. Sanarwar ta kara da cewa wata mota ce makare da ababen fashewa ta tarwatse a wani wuri kusa da shingen jami'an tsaro dake kauyen Ber a yankin Timbuktu, fashewar da nan take ta janyo mutuwar ma'aikatan su 2.
Duk dai da irin wadannan hare-hare da jami'an MINUSMA ke fuskanta, sanarwa ta ce MDD ba zata dakatar da baiwa kasar Mali tallafin da ya dace ba.
Idan dai za a iya tunawa a ranar 25 ga watan Afirilun da ya gabata ne kwamitin sulhun MDD, ya baiwa tawagar MINUSMA ikon jagorantar ayyukan wanzar da zaman lafiya a Malin, tun kuma farkon watan Yuli kawo wannan lokaci jami'an wannan tawaga ke fuskanatar hare-hare akai akai daga mayakan 'yan awaren kasar.(Saminu Alhassan)