Manazarta harkokin wasan kwallon kafa dai na ganin dan wasan bayan, wanda ya ci wa kungiyar kasar sa ta Girka kwallaye 4 a wasanni 16 da ya buga ma kungiyar, ya kasance a kulaf din Schalke tun a shekara ta 2010, ya kuma ciwa kulaf din kwallaye 3 a wasanni 61 da ya buga.
Da yake tsokaci game da batun dakko dan wasan, daraktan kulaf din na Bayer Leverkusen Rudi Voller, cewa ya yi sauri da iya sarrafa kwallo da ka, tare da himmar cimma nasara da dan wasan ke da shi, sun sanya shi kasancewa irin dan wasan da suke farin cikin samu a yanzu. Voller ya kara da cewa zuwan Papadopoulos kulaf din su, zai basu damar kara inganta tsaron gida yadda ya kamata.
A kakar wasannin data gabata dai kulaf din na Leverkusen ya kammala wasannin sa ne da kasancewa a matsayi na 4, a teburin gasar zakarun kasar Jamus ta Bundesliga.