in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Real Madrid ta samu mai tsaron gidan Levante Navas
2014-08-07 19:57:20 cri
Mahukuntan kulaf din Real Madrid sun ce sun kulla wata kwangila ta shekaru 6, da mai tsaron gidan Levante na yanzu Keylor Navas, a Lahadi 3 ga watan nan.

Wannan kwangila dai zai ta sanya dan Costa Rica fara taka leda a Real Madrid har zuwa lokacin da za a kammala gasar cin kofin zakarun Turai a shekarar 2020, haka kuma an ce Madrid din ta sayi wannan dan wasa ne kan kudi kimanin dala miliyan 13 kafin a kammala yarjejeniyar sakin sa.

Kammala wannan musayar kulaf da Navas ya yi zai sa shi bayyana a filin wasan Santiago Bernabeu na kulob din Real Madrid a ranar Talata.

Navas ya kasance daya daga cikin 'yan wasa 3 da Real Madrid ta kulla kwangila tare da su a wannan lokaci na bazara, lamarin da ya sanya kudaden da kulof din ya kashe kaiwa kimanin Euro miliyan 130, ana kuma sa ran karuwar wannan adadi, kafin fara buga wasannin wannan kaka, idan har Radamel Falcao na kulob din Monaco shi ma ya koma Real Madrid.

Har wa yau kuma, shigowar Navas Real Madrid, da kuma la'akari da irin rawar ganin da ya taka a matsayin mai tsaron gida a gasar cin kofin duniya da ta gudana a kasar Brazil, manuniya ce dake haskaka cewa daya daga masu tsaron gidan Real Madrid Iker Casillas, ko kuma Diego Lopez zai yi sallama da kulaf din nan da dan lokaci.

A baya dai kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya ce Casillas zai buga wasannin European Supercup da kulaf din zai buga, sai dai ya ce bai san abun da zai biyo bayan wannan gasa ba game da makomar mai tsaron gidan. A hannu guda kuma, gazawar da Casillas din ya nuna ya yin wasan da Manchester United ta doke Real Madrid da ci 3 da 1 a ranar 2 ga watan nan, shi ma ya sanya wasu bayyana shakku kan dorewar golan Real Madrid.

Shi kuwa Lopez wanda ya taba taka leda a matsayin mai tsaron gida na farko ga kungiyar ta Madrid a kakar wasanni da ta gabata, ana ganin zai samu gayyato zuwa wani kulaf dake buga Premier League ko MLS na kasar Amurka. Don haka dai abu ne mawuyaci ya ci gaba da zama a Real Madrid a matsayin mai tsaron gida na 3.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China