Wannan dai nasara da Mozambique ta samu kan Tanzania a birnin Maputo, ya ba ta damar dara Tanzania da tazarar maki 4 da 3, za ta kuma buga zagayen wadannan wasanni na biyu.
Dan wasan Mozambique din Josemar ne dai ya ci wa kulaf din na sa kwallon farko, ana daf da tafiya hutun rabin lokaci, kafin a farke ta, kana Mozanbique din ta samu damar kara kwallo ta 2.
A cewar kocin kungiyar ta Mozambique Joao Chissano, sun sadaukar da wannan nasara da suka samu ga al'ummar kasar wadanda ke baiwa kungiyar cikakken goyon baya a ko da yaushe.
Shi kuwa a nasa bangare kocin Tanzania Mart Nooij, wanda a baya ya taba horas da kungiyar Mozambique, cewa ya yi dan wasan Mozambique Elias Pelembe Domingues, ya baiwa kungiyar sa gagarumin taimako a nasarar da kulaf din sa ya samu a wancan wasa.
A takaice dai Nooij ya ce 'yan wasan Mozambique sun taka rawar gani wajen dorewar nasarar da suka samu a wannan wasa.