Albarkacin ranar giwaye ta duniya, da ake bikinta ko wace ranar 12 ga watan Agusta, masu kare namun daji sun dauki niyya a ranar Litinin a Nairobi wajen dukufa ga karfafa matakan yaki da farauta namun daji ba bisa doka ba, tare kuma da fadakar da duniya kan halin da giwaye suke ciki a Afrika.
Kungiyar kare namun dajin Afrika (AWF) da WildlifeDirect, da wasu kungiyoyin kare muhalli biyu, sun bayyana a Nairobi cewa, za su yi aiki tukuru tare gwamnatoci da kuma hukumomin da abin ya shafa wajen daidaita ayyukansu tare domin kare giwaye a nahiyar Afrika. Wadannan kungiyoyi sun bayyana cewa, a yanzu haka akwai giwaye dubu dari biyar a nahiyar Afrika, sabanin giwaye miliyan 1.2 da ake da su a wajajen shekarar 1980. Giwaye dubu ashirin da biyar zuwa dubu talatin da biyar masu farautar namun daji ba bisa doka ba suke kashewa a kowace shekara a Afrika domin amsa bukatun hauren giwa daga kasashen duniya, musammun ma daga yankin Asiya. (Maman Ada)