Yawan giwayen da ke zama cikin daji a Afirka ya ragu da kashi 2 cikin kashi 3 a shekaru 10 da suka wuce
Ranar 26 ga wata, asusun kula da harkokin dabbobin daji na kasa da kasa wato WWF ya bayyana a birnin Brazzaville, hedkwatar kasar Congo (Brazzaville) cewa, bisa sakamakon bincike mai dumi-dumi da aka samu, an ce, yawan giwayen da ke zama cikin daji a kasashen Afirka ya ragu da kashi 2 cikin 3 a cikin shekaru 10 da suka wuce sakamakon farautarsu da yawa a asirce.
Wani jami'in asusun WWF a yankin tsakiyar Afirka ya yi wa kafofin yada labaru bayani a wannan rana cewa, yanzu wasu gungun dakaru na kasa da kasa suna jan gorar aikace-aikacen farautar namun daji masu wuyar samuwa.(Tasallah)