in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama masu fataucin hauren giwa Sinawa a Kenya
2014-02-10 13:30:47 cri

Mahukunta a ofishin kula da gandun daji na kasar Sin a ranar Litinin din nan suka tabbatar da cewa, an kama wani Basine da ake zargi da fataucin hauren giwa a kasar Kenya bayan wani aikin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Wanda ake zargin mai suna Xue, mahukuntar kasar Kenya suka kama shi a ranar 17 ga watan Janairu a Nairobi, babban birnin kasar ta Kenya, sannan suka mika shi a nan kasar Sin ga mahukuntar da abin ya shafa kashegari, abin da ya zama karo na farko da kasar Sin ta damke mai keta dokan gandun daji a kasashen waje.

Xue dai an ce yana jagorantar wata kungiya dake fataucin hauren giwaye ne a kasar Kenya na tsawon lokaci inda yake daukan hayar masu jigilar hauren zuwa kasar Sin.

Sauran wadanda ake zargin mutane biyu masu suna Zheng da Li su kuma an kama su a ranakun 16 da 17 ga watan na Janairu lokacin da suke kokarin shiga kasar Sin. Ya zuwa yanzu, duk wadanda ake zargin suna tsare.

Wannan kame dai na daga cikin ayyuka mai lakabin "Cobra 11" da kasar Sin tare da sauran kasashen Asiya suka kaddamar da hadin gwiwwar kasashen Afrika da arewacin nahiyar Amurka domin hana laifuffukan cin zarafin namun daji tun daga karshen shekarar ta 2013 har zuwa farkon bana. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China