Mataimakin babban manajan kamfanin wanda ke kusa da dandalin Waza a Arewacin kasar Mr. Lan Ronghe, shi ne ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua hakan. Mr. Lan ya kara da cewa ma'aikacin ya samu kulawar gaggawa daga tawagar likitocin sojin kasar ta Kamaru sakamakon harbi biyu da aka yi masa, kafin daga bisani a garzaya da shi babban asibitin birnin N'djamena na kasar Chadi domin samun karin kulawar kwararru.
Mr. Lan ya ce ma'aikacin ya zubda jini mai yawa, ga kuma rashin kyan hanya, wanda hakan ya tsawaita lokacin da aka shafe kafin kai shi ga Asibitin kawancen gwamnatocin Chadi da Sin dake Chadin.
Game da yanayin da wannan ma'aikaci yake ciki kuwa, Mr. Lan ya ce likitocin suna da karfin gwiwar zai rawu, muddin dai ba a ci karo da wata matsala game da yanayin jikin nasa nan da 'yan sa'o'i ba. (Saminu Alhassan)