A alhamis din nan 7 ga wata, kakakin kwamitin kiwon lafiya da kayyade yara haihuwa na kasar Sin, Song Shuli ya bayyana a gun taron manema labaru cewa, Sin ta gabatar da shirin share fage da ba da jiyya ga cutar Ebola, inda aka tabbatar da ba da jiyya da rahoto dangane da cutar Ebola, tare da bukatar hukumomin likitanci a wurare daban daban da su ba da rahoto cikin awa biyu kai tsaye idan suka samu wani mai dauke ko wadanda ake tababa cewa sun kamu da cutar Ebola.
Mr Song ya bayyana cewa, kawo yanzu babu wanda ya kamu da cutar a nan kasar Sin don haka a kokarin kauracewa yaduwar cutar cikin kasar, da ba da kariya ga lafiyar mutanen da suka kai ziyara a wuraren da cutar ke yaduwa, hukumomin da abin ya shafa suna aiki sosai.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya, wato WHO ta yi hasashen cewa, cutar Ebola ba za ta yadu zuwa sauran nahiya cikin sauki ba.(Fatima)