Kenya dai ta rasa damar shiga jerin kasashen da za a fafata da su a wannan gasa ta Morocco ne, bayan da Lesotho ta lashe ta a wasa na biyu da suka buga. A wasan farko da kasashen biyu suka fafata dai, sun tashi kunnen doki ne maras ci da Lesotho, kafin daga bisani a wasa na biyu Lesotho ta jefawa Kenya kwallo daya mai ban haushi.
Hakan dai na nuna cewa Kenya ba za ta buga manyan wasannin kasa da kasa ba har tsahon shekaru 2, ya zuwa wasannin share fagen gasar cin kofin nahiyar Afirka na shekarar 2017.
A takaice dai a iya cewa wannan rashin nasara da Kenya ta hadu da shi, ita ce ta janyo korar kocin ta dan asalin kasar Belgium, wanda ya karbi aikin horas da 'yan wasan Kenyan tun cikin watan Fabarairun shekarar 2013 da ta gabata. A baya dai kocin ya taba horas da 'yan wasan kasar Burindi daga shekarar 2007 zuwa 2012. Ya kuma jagoranci Kenya a manyan gasanni biyu da ta buga, wadanda duka suka gaza cimma nasara a cikin su.
A wani ci gaban kuma kyaftin din kulaf din na Kenya Victor Wanyama, ya baiwa al'ummar kasar hakurin rashin nasarar su a hannun Lesotho. A cewar Wanyama, duk da kokarin da suka yi na ganin sun samu nasara a wasan na biyu, hakar su ta ci tura, don haka a cewar sa wannan wani rashin sa'a ne da ya same su, wanda kuma hakan ya baiwa Lesotho damar shiga jerin kasashen da za su buga zagaye na gaba a rukuni na uku, tare da Burkina Faso, da Angola da kuma Gabon, a yunkurin shiga jerin kasashen da za su halarci gasar AFCON ta badi.