in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude wasannin kungiyar Commonwealth karo na 20 a Glasgow
2014-08-01 09:42:30 cri

An bude wasannin gasar kasashe renon Ingila na Commonwealth karo na 20 a daren ranar Laraba 23 ga watan nan a birnin Glasgow na kasar Scottland. Kamar yadda sashen masu daukar bakuncin wasannin na wannan karo suka bayyana, an yi bikin bude gasar cike da shagulgula na al'adun gargajiyar kasar Scottland.

An gudanar da bikin bude wasannin kungiyar ta Commonwealth karo na 20 ne dai a filin wasa na kungiyar wasan kwallon kafar Celtic ta kasar Scottland din, bikin da Saurauniyar Birtaniya Elizabeth II ta halarta.

Babban ministan gwamnatin kasar Scottland Alexander Salmond ya bayyana cewa, ana sa ran yawan kudin da za a kashe a wasanni zai kai Fam miliyan 575, kashi 80 cikin dari na wannan kudi kuwa sun fito ne daga gwamnatin kasar Scottland, sai kuma kashi 20 cikin dari daga gwamnatin birnin Glasgow.

'Yan wasa kimanin dubu 5 daga kasashe da yankuna 53 na kasashe renon Ingila ne dai ke halartar wannan gasa ta bana. Ana kuma fafatawa a wasanni 17. Kana ana fatan rufe wasannin na wannan karo ne a ranar 3 ga watan Agustar dake tafe. (Zainab)

Shelley da Daniel sun lashe lambar zinari a gasar gudun famfalaki

A ranar Lahadin karshen makon jiya ne dan wasan gudun famfalakin kasar Australian Michael Shelley, ya lashe lambar zinari ajin maza, a gasar kasashe renon Ingila ta commonwealth karo na 20 da ake ci gaba da gudanarwa yanzu haka a birnin Glasgow na kasar Scotland, yayin da ita kuma Flomena Cheyech Daniel daga Kenya, ta samu nasarar lashe lambar zinari a ajin mata.

Shekaru 4 da suka gabata dai Shelley mai shekaru 30 da haihuwa, ya samu lambar azurfa a gasar da ta gudan a birnin Delhi, ya kuma zo na 16 a gasar wasannin Olympics ta London. Inda a wannan karo ya kammala gudun kilomita 5, cikin sa'oi 2 da mintuna 11 da dakoki 15. Sakamakon da ya zame masa mafi girma a tarihin gasannin da ya shiga.

Shi kuwa Stephen Chemlany na Kenya, wanda a wannan karo ya samu lambar yabo ta azurfa, a shekarar 2011 ma ya lashe wannan lamba a birnin Berlin, inda a wannan karo ya kammala gudunsa da tazarar mintuna 43 tsakanin sa da wanda ke a matsayi na farko.

Cikin wadanda suka samu nasara a wannan gasa dai akwai Philip Kiplimo daga Uganda, wanda ya zo na 3, nasarar da ta baiwa kasar sa damar samun lambar yabo irin ta ta farko a wannan gasa ta gudun fanfalaki a gasar ta Commonwealth.

Ita kuwa Flomena Cheyech Daniel, wadda ta lashe lambar zinari ajin mata, ta kammala gudun ta ne cikin sa'oi 2 da mintuna 26 da kuma dakika 45, yayin da Caroline Kilel ke biye cikin sa'oi 2 da mintuna 27 da dakika 10. A kuma matsayi na 3 akwai Jess Trengove daga Australia, wadda ta kammala na ta gudun cikin sa'oi 2 da mintuna 30 da dakikoki 12.

Da take bayyana jin dadin ta game da wannan gagarumar nasara da ta samu ta lashe babbar lambar yabo a gasar ta bana, Shelley ta ce ta samu karin gogewa. Ta kuma ce lashe wannan lamba babban abun alfahari ne gare ta. "Na yi iyakacin kokari wajen ganin ban baras da dama ta kamar yadda na yi a baya ba" batu ne ake yi na yin iyakacin kokarin gudu iya iyawarka, har yanzu ina ganin wannan nasara da na samu tamkar mafarki" a kalaman Flomena Cheyech Daniel. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China