in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana samun karuwar fadace-fadace yayin wasannin kwallon kafa a kasar Italiya
2014-07-23 18:12:38 cri
Wani bincike da kamfanin dillancin labarai na ANSA ya fitar, ya nuna yadda ake samun karuwar rigingimu da kan barke tsakanin 'yan kallo da jami'an tsaro, yayin wasannin kwallon kafar ajin kwararru na kasar Italiya.

Binciken da ANSA ya yi dai ya nuna karuwar alkaluman irin wadannan rigingimu da kaso 37 bisa dari a kakar wasanni ta 2013 zuwa 2014, idan an kwatanta da na kakar wasannin da ta gabace ta.

Kaza lika wannan kakar wasannin ta gamu da artabu da dama, musamman yayin wasannin ajin kwararru na Seria A, wanda wancan bincike ya nuna cewa yawan raunukan da 'yan kallo suka samu yayin wasannin ya karu da kaso 35 bisa dari, yayin da 'yan sandan kwantar da tarzoma suka samu raunuka da yawan su ya karu da kaso 80 bisa dari, idan an kwatanta da na kakar wasannin ta shekarar 2012 zuwa 2013. Baya ga batun raunuka sakamakon arangamar 'yan sanda da 'yan kallo, a kwai kuma rahotanni na rasa rayuka, inda a ranar 3 ga watan Mayun da ya gabata ma wani matashi mai suna Ciro Esposito dake goyon bayan kungiyar Napoli ya rasa ransa, sakamakon raunukan da ya samu, bayan da wani magoyin bayan kungiyar Roma ya harbe shi, gabanin wasan karshe na cin kofin "Italian Cup".

A hannu guda akwai matsalar 'yan banga dake da karfi kwarai a harkar wasanni, musamman na kwallon kafa a kasar. Wasu alkaluma sun nuna cewa magoya bayan irin wadannan kungiyoyi na 'yan daba sun kai mutane 4,000 a kasar, wadanda kuma kan shirya fadace-fadace ta hanyar amfani da dandalin yanar gizo.

A cewar shugaban kulaf din Napoli Gennaro Di Tommaso, barazanar irin wadannan bata-gari ta karade wannan fage na wasanni, ta yadda suke hana nishadantuwa da shi kan sa wasan, suna kakabawa harkar matsaloli iri daban daban, ta yadda babu wani tabbas na samun yanayin kwanciyar hankali da lumana a harkar kwallon kafa a cikin kasar.

Tommaso ya ce a yanzu haka babu wani tabbas game da batun kisan Ciro Esposito, wanda tun bayan da ya rasu ake zaman dar dar, duba da yadda wasu rahotannin ke cewa, magoya bayan kungiyar Napoli na shirin daukar fansar kisan sa.

Hukumomi da jami'an tsaro dai na iyakacin kokarin ganin sun dakile fadace-fadace masu alaka da wasannin kwallon kafa, ta hanyar tsaurara matakan tsaro a filayen wasanni, da amfani da tikiti na musamman domin gane 'yan kallo masu tada fitina yayin wasanni, sai dai ga alama har yanzu akwai sauran rina a kaba, game da cimma wannan buri na mahukuntan, duba da yadda kusan duk sati sai an samu aukuwar wadannan matsaloli na fadace-fadace.

Masu fashin baki dai na ganin wannan matsala da Italiya ke fuskanta, babban koma baya ne ga harkar wasan kwallon kafar kasar. A cewar wani lauyan harkokin kwallon kafa dake kasar Lorenzo Contucci, kulaflikan Italiyan na can baya, idan an kwatanta su da takwarorin su na sauran kasashen turai kamar Jamus da Ingila. Contucci ya ce in ban da filin wasa na kulaf din Juventus, ragowar filayen wasan kasar na karkashin gundumomi ne, wadanda ba sa taka wata muhimmiyar rawar gani wajen tabbatar da tsaro, sabanin abin da ke faruwa a sauran sassan nahiyar ta Turai.

Wani ma rahoto da kamfanin dillancin labarai na ANSA ya fitar, ya nuna cewa matsakaicin yawan kujerun kallon wasa da a kan sayar da su a filayen wasan kasar Jamus ya kai kaso 80 bisa dari, sabanin takwarorin su na Italiya da ke da kaso 40 bisa dari, sakamakon matsalolin tsaro da suka dakushe martabar kwallon kafar kasar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China