Kroos dai ya taka muhimmiyar rawa wajen lashe gasar cin kofin duniya da Jamus ta samu nasarar sa a 'yan kwanakin baya, an kuma zabe shi a matsayin dan wasa mafi hazaka a shekarar 2007, lokacin da Jamus ta kasance a matsayi na uku, a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya, na matasa 'yan kasa da shekaru 17. Ya kuma fara bugawa Bayern Munich kwallo yana dan shekaru 16. Kuma kulaf din na Bayern ya taba bada aron sa ga Bayer Leverkusen, kafin daga bisani ya sake komawa Munich.