in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kulaf din kasar Jamus ya haye matsayi na daya a jadawalin FIFA na watan Yuli
2014-07-23 18:11:00 cri
Kulaf din kwallon kafar kasar Jamus ya haye matsayi na daya, a jadawalin hukumar gudanar da kwallon kafa ta duniya FIFA, bayan da ya samu nasarar lashe gasar cin kofin duniya da aka kammala a kwanakin baya a kasar Brazil.

Kulaf din na Jamaus dai wanda nasarar da ya samu ta wannan karo, ta sanya shi daukarwa kasar ta Jamus kofin na duniya a karo na hudu, bayan shafe shekaru kusan 20 raban sa da ya dauki kofin, ya tashi daga matsayin da yake kai na 2 zuwa matsayi na daya, sai kuma kasar Argentina da ke biye a matsayi na 2, ya yin da Netherlands ke a matsayi na 3.

Sauran kasashen da suka daga zuwa matsayi na sama a jadawalin da FIFAr ta fitar a baya bayan nan sun hada da Colombia daga na 8 zuwa na 4, da Belgium daga 11 zuwa na 5, da Faransa daga na 17 zuwa na 10, da da kuma Costa Rica da ta daga daga matsayi na 28 zuwa na 16.

A daya hannun kuma, kasashen da tauraruwar su ta disashe a wannan fage sun hada da Sifaniya, wadda ta fado daga matsayi na 1 zuwa na 8, sai Portugal da ta sauko zuwa na 11 daga na 4, da Italiya daga na 9 zuwa na 14, da Ingila da ta fado na 20 daga matsali na 10. Ita ma mai masaukin bakin gasar ta bana wato kasar Brazil ta sakko daga matsayi na 3 zuwa na 7.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China