in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO da kasashen yammacin Afrika za su kaddamar da shirin tunkarar barkewar Ebola
2014-08-01 14:24:09 cri

Babbar darektar hukumar lafiya ta duniya WHO da shugabannin kasashen dake Afrika ta yamma, wadanda barkewar cutar Ebola ya shafa, za su yi wani taro a kasar Guinea domin kaddamar da wani sabon shirin dalar Amurka miliyan 100 domin tunkarar cutar.

Babbar darektar hukumar lafiya ta duniya, Margaret Chan, ta bayyana a cikin wata sanarwa cewar, karfin yaduwar cutar da kuma tasirin barazanar cutar, ya sa dole ne hukumar lafiya ta duniya da bukaci kasashen Guinea, Liberia da Saliyo su kara kaimin matakan da suka dauka, ya zuwa wani mataki na gaba wanda ke bukatar karin kudade da kuma samar da kwarewa na tunkarar cutar da kuma inganta matakan gudanarwa da daura damarar yankin, domin tunkarar cutar ta Ebola mai saurin kashe jama'a.

Shirin gaggawa na tunkarar cutar ta Ebola a Afrika ta yamma, ya gano cewar, akwai bukatar kara samar da ma'aikata da za'a tura zuwa kasashen dake fama da cutar domin a kawo karshen matsalar rashin isassun ma'aikata da kayayyakin aiki wajen yaki da cutar. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China