in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barkewar Ebola ta zamanto barazana ga Britania, in ji sakataren harkokin wajen kasar
2014-07-31 10:33:37 cri

Sakataren harkokin waje na Britania Philip Hammond, ya ce, cutar Ebola wacce ta hallaka daruruwan mutane tun daga farkon watan Fabrairun wannan shekarar, na iya zamantowa barazana ga kasar Britania.

Philip Hammond, ya bayyana hakan ne a yayin da ya shugabanci wani taro na gaggawa na kwamitin Cobra, wanda aka kafa domin Britania ta dauki matakai na tunkarar samar da kariya na haramta yaduwar kwayar cutar ta Ebola a Britania.

Sakataren harkokin wajen ya ce, kawo ya zuwa yanzu, babu wani 'dan asalin Britania da ya kamu da cutar, kuma babu wani rahoto na barkewar cutar a kasar, to amma ya ce, gwamnatin kasar na kallon barkewar cutar a matsayin wani babban abu da ke bukatar tsauraran matakai.

Kawo ya zuwa yanzu, mutane 670 sun rasa rayukansu a yammacin Afrika a sakamakon barkewar cutar (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China