in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeriya ta dakatar da jirgin da ya shigo da mai dauke da Ebola kasar
2014-07-30 10:08:27 cri

Gwamnatin Nigeriya ta dakatar da zirga-zirgar jirgin saman Asky Airline wanda ya shigo da wani 'dan Liberiya mai dauke da cutar Ebola kasar. Mukaddashin babban darektan hukumar kula da zirga-zirgan jiragen saman kasar NCAA Benedict Adeyileka ya sanar da wannan mataki a jihar Ikko ranar Talatan nan.

Mr. Benedict Adeyileka ya yi bayanin cewa, an yi hakan ne domin kare al'ummar kasar daga kamuwa da cutar ta Ebola mai kisa nan take da yanzu haka ya harbu a wassu sassa na kasashen Afrika yana masu barna.

Asky Airline dai tana zirga-zirga ne tsakanin kasashen gabashi, yammaci, da tsakiyar Afrika, kuma tana yada zango zuwa Abuja da jihar Ikko sau 80 a kowace mako. Jirgin a makon da ya gabata ne ta shigo da wani 'dan asalin kasar Liberiya zuwa jihar Ikko, alhalin yana dauke da cutar wanda yanzu haka ya mutu.

Hukumar kula da zirga-zirgan jiragen saman na Nigeriya ta bukaci manajan kamfanin jiragen na Asky a Nigeriya da ya yi bayanin dalilin shigowa da mai dauke da wannan cuta, amma ba ya da wani takamaiman dalili a kan hakan, don haka Mr. Benedict Adeyileka ya ce, tun da manajan bai nuna wani kokarin hana irin wannan laifi ba, ko ma dauko fasinjoji masu kamuwa da wannan cuta ta Ebola zuwa Nigeriya, aka dauki wannan mataki. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China