A cikin wata sanarwar da ya bayar a ranar talatan nan 29 ga wata, kamfanin ya bayyana cewa, kamfanin jiragen saman kasar Togo ya amince da ajiye na'uran auna zafin jikin mutum a filin jiragen sama dake birnin Lome don hana shigowar fasinjojin da zafin jikinsu bai yi daidai ba.
A ranar 25 ga wata, jirgin saman ya dauko wani fasinja dan asalin kasar Liberia a filin jiragen sama dake birnin Lome zuwa jihar Ikko a tarayyar Nijeriya, wanda aka zargin yana dauke da cutar Ebola, daga bisani ya muta a wani asibiti mai zaman kansa a jihar.
Bisa sabuwar sanarwar da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta bayar, an ce, ya zuwa ranar 20 ga watan Yuli, yawan mutane daga kasashen Guinea, Liberia da Saliyo da aka tabbatar da ko zarginsu da kamuwa da cutar Ebola ya kai 1093, kuma 660 daga cikinsu sun mutu. (Zainab)