in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala atisayen soja na RIMPAC-shekarar 2014 a tekun Pacific
2014-08-02 16:45:19 cri

Ranar 1 ga wata da safe bisa agogon jihar Hawaii ta kasar Amurka, an kammala atisayen soja na RIMPAC-shekarar 2014 a jihar yadda ya kamata.

Kasashe 22 sun tura jiragen ruwan soja fiye da 40 da jiragen sama fiye da dari 2 tare da sojoji kimanin dubu 25 don shiga wannan atisayen soja na karo na 24, inda kasar Sin ta tura jiragen ruwan soja 4, jiragen sama masu saukar ungulu 2 da kuma sojoji fiye da 1100.

Atisayen soja na RIMPAC-shekarar 2014 da aka yi a yankin teku da ke dab da tashar jiragen ruwa na Pearl a jihar Hawaii, atisayen soja ne na kasa da kasa da hedkwatar rundunar jiragen ruwan tekun Pacific karkashin shugabancin rundunar sojojin ruwan kasar Amurka take shiryawa sau daya a shekaru biyu-biyu. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China