Shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya gana da ministan harkokin wajen Sin Mista Wang Yi a ran 22 ga wata a birnin Algiers, babban birnin kasar Aljeriya.
A ganawarsu, Mista Bouteflika ya bayyana cewa, har abada kasar Aljeriya ba ta manta goyon bayan ta samu daga kasar Sin ba a cikin dogon lokaci. Kasar Sin ta kasance abokiyar Aljeriya da ke ba ta taimako. Aljeriya tana son yin kokari tare da Sin, don kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin bangarorin biyu, da kara samun kyakkyawan sakamako daga bunkasuwar dangantakar da ke tsakaninsu.
A nasa bangare, Mista Wang Yi ya ce, shugaba Bouteflika shi ne tsohon aboki mai kirki na jama'ar kasar Sin, wanda ya bayar da gudummawa matuka wajen kafuwar dangantaka a tsakanin Sin da Aljeriya, da kuma maido da halaliyar kujerar Sin a MDD, sakamakon hakan kuma jama'ar kasar Sin sun nuna girmamawa. Wang ya kara da cewa, Sin tana mai da hankali sosai kan muhimmin matsayin kasar Aljeriya da amfanin da take bayarwa, Sin tana son kara hadin kai da kasar Aljeriya a harkokin duniya da shiyya-shiyya, da kuma kare moriyar kasashe masu tasowa tare.(Danladi)