in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jakadan Sin dake Najeriya ya kira taron kamfanonin Sin dake Najeriya
2014-07-26 16:50:52 cri

Jakadan kasar Sin dake Najeriya ya kira wani taron musamman na kamfanonin Sin dake gudanar da harkokinsu a Najeriya a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, a Jumma'a 25 ga wata.

A wajen taron, wakilan kamfanonin sun takaita ayyukan da suka yi a farkon watannin 6 na bana. Har wa yau kuma, Jakadan kasar Sin dake Najeriya mista Gu Xiaojie ya yi kira ga kamfanonin Sin da su dora muhimmanci ga ingancin aiki da samun amincewa daga al'ummar kasar, da kokarin samar da wani yanayi mai kyau a fannonin tsaro, ra'ayin jama'a, da zaman al'umma, don taimakawa hadin gwiwar bangarorin 2 ta fuskar tattalin arziki da cinikayya.

Haka zalika, Jakada Gu ya jaddada bukatar samar da ayyukan da za su yi amfani ga rayuwar jama'ar kasar Najeriya, gami da bukatar kamfanonin Sin da su yi kokarin tabbatar da tsaron ma'aikatansu.

A wajen taron kuma, karamin jakadan Sin mai kula da harkokin kasuwanci, mista Zhou Shanqing, ya ce, yawan musayar ziyara tsakanin manyan jami'an gwamnatocin kasashen Sin da Najeriya da aka samu a shekarun baya, ya aza harsashi mai kyau ga ci gaban hadin kai tsakanin bangarorin 2, sai dai a nan gaba, ya kamata a kara mai da hankali kan wasu matsalolin da kamfanonin Sin suke fuskanta a Najeriya, don daidata su yadda ake bukata. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China