140715murtala
|
Yayin da ta ke ganawa da wasu daga cikin iyayen 'yan matan Chibok din da aka sace sama da watanni uku da suka gabata, Malala ta ce ta fahimci irin yadda suke ji a zukatansu, kuma tana fatan 'yan matan su kusan dari 3 za su dawo ga iyalan nasu lami-lafiya.
A ganawarta da shugaba Goodluck Jonathan kuwa, Malala ta yi kira ga gwamnatin tarayyar kasar, da ta kokarta kubutar da wadannan 'yan mata na Chibok cikin hanzari.
Ya zuwa yanzu dai babu duriyar 'yan mata da 'yan Boko Haram suka sace daga jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar. Tuni kuma wasu daga cikin iyayen 'yan matan suka kafa wata kungiya mai taken "Bring Back Our Girls", wadda ke da rajin kiga da a kubutar da 'yan matan. Kungiyar kuma ta rika gudanar da gangami a Abuja, domin kalubalantar gwamnatin tarayya, da ta ceto 'yan matan 'yan makaranta. (Murtala)