in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rahoto: An fi samun matsalar satar mai a Najeriya
2014-07-12 16:22:18 cri
Wani shafin yanar gizo na kasar Birtaniya "Oilprice.com" ya gabatar da wani rahoto a kwanakin baya kan yadda ake aikata laifin satan mai a kasashe daban daban, inda aka bayyana cewa kasashe biyar wato Najeriya, Mexico, Iraki, Rasha, da Indonesia kasashe ne da suka fi fama da wannan matsala. Sai dai daga cikinsu, an ce matsalar satar mai a Najeriya ta fi kamari, da kuma yawan janyo asara.

Rahoton ya ce, ana satar mai kimanin ganguna dubu 400 a ko wace rana a kasar Najeriya, lamarin da ya sanya kasar na asarar dalar Amurka miliyan 1700 a ko wane wata, kwatankwacin kashi 7.7% na yawan GDP din na kasar, wanda adadin ya haura kudin da kasar ke zubawa harkokin ilimi da kiwon lafiya. Wannan adadi, a cewar rahoton, ya nuna yadda gwamnatin Najeriya da manyan kamfanonin mai na kasa da kasa suka rasa abin da za su yi dangane da wannan matsala. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China