Ramtane Lamamra, ministan harkokin waje na kasar Algeria ya bayyana a yayin bikin kaddamar da taron, cewar a halin yanzu dai, duniya na cikin wani hali na rudani, kasashe da dama na tinkarar hare-haren ta'addanci, da na manyan laifuffukan kasa da kasa a sassa daban daban na duniya. Dalilin haka ne, ya kamata kasashe membobin kungiyar 'yan ba ruwanmu su dauki matakai don inganta hadin gwiwarsu, a kokarin ciyar da irin wannan sabon sauyin da aka samu a cikin dangantaka a tsakanin kasa da kasa.
Mr. Lamamra ya jaddada cewa, kungiyar 'yan ba ruwanmu ta samar da wata kyakkyawar dama ga kasashe masu tasowa wajen cudanya a tsakaninsu, a matsayin wata dama inda kasashe masu tasowa suke iyar cimma matsaya daya kan dimbin lamura, da kuma yin shawarwari tare da kasashe masu ci gaba cikin adalci.
A tsawon taron, kasashe membobin kungiyar da ministoci da jami'ai da kuma kwararru na kasashe 'yan kallo za su mai da hankali kan batutuwan da ke jawo hankulansu a fannonin siyasa, tattalin arziki da kuma tsaro tare da fitar da wata sanarwar karshe. (Kande Gao)