Kamfanin zirga-zirgar jirgin saman Algeria ya bayyana cewa, wannan jirgin saman mai samfurin "MD83" ya dauke da fasinjoji 110 daga kasashe da dama. Kafin ya bace, jirgin saman yana kusa da iyakar kasar Algeria. Amma sabo da yanayi mara kyau, aka bukaci matukan jirgin saman da su canza hanya domin kauracewa yin karo da wani jirgin na daban tun daga nan kuma ba a sake jin duriyar sa ba.
Kawo yanzu dai, kamfanin zirga-zirgar jiragen saman Algeria ya riga ya kaddamar da shirin gaggawa domin fara aikin neman jirgin.(Fatima)