in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya yi wa Abdelaziz Bouteflika murnar sake zama shugaban Algeria
2014-04-20 17:17:37 cri

Ranar Asabar 19 ga wata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya taya shugaba mista Abdelaziz Bouteflika murnar sake darewa kujerar shugabancin kasar Algeria.

A cikin sakon murnar da ya aike, shugaba Xi ya ce, kasashen Sin da Algeria suna da zumunta mai karfi a tsakaninsu. A cikin shekaru 55 da kafa huldar diplomasiyya a tsakaninsu, har kullum suna kasancewa aminai kuma 'yan uwa. A watan Fabrairu na shekarar da muke ciki, kasashen 2 sun sanar da kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu daga dukkan fannoni, lamarin da ya bayyana kyakkyawar huldar da ke tsakanin Sin da Algeria, haka kuma ya samar da kyakkyawar makoma wajen kara raya huldar da ke tsakanin kasashen 2.

Shugaba Xi ya kara da cewa, yana mai da hankali kan bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da Algeria, tare da fatan hada kai da shugaba Abdelaziz Bouteflika wajen kara inganta da bunkasa huldar abokantaka a tsakanin kasashen 2 bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni, a kokarin kawo wa kasashen 2 da jama'arsu alheri.

Ranar 18 ga wata, gwamnatin Algeria ta sanar da cewa, mista Abdelaziz Bouteflika ya samu nasarar sake zama shugaban kasar bayan lashe babban zaben kasar da aka gudana. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China