A ranar Talata 30 ga wata, sojin Najeriya ta dorawa kamfanonin mai na Shell da Agip laifin asarar man fetur da yawansa ya kai ganga 190,000 kowace rana a filayen hako mai dake jihar Bayelsa a kudancin kasar.
Wannan asara ya sa an samu raguwar kudin shiga a jihar inda yayi kasa daga naira biliyan 12.4 a watan Mayu zuwa naira biliyan 9 a watan Yuni, bisa kididdiga ta wata wata da gwamnan jihar Seriake Dickson ya bayar.
Kamfanonin man guda biyu sun nuna kasawarsu a wajen samar da mai a nau'rorinsu dake jihar Bayelsa domin su wanke kansu daga dukkan wani nauyi a bangaren masu sayen danyen mai. Sun kuma bayyana cewa an samu wannan koma baya ne saboda yadda ake satar mai a jihar.
A nasa bangare, mai magana da yawun hukumar tsaro ta hadin gwiwa a yankin Niger Delta (JTF), Onyema Nwachukwu yace da kamfanonin sun bi shawarar rahotanni da hukumar ta ba su, da hakan bai auku ba.(Lami Ali)