140724-hukumar-fifa-ta-cire-takunkumin-da-ta-sanyawa-NFF-Bello
|
Kakakin hukumar kwallon kafa ta Najeriya Ademola Olajire ne dai ya sanar da haka, inda ya ce babban sakataren hukumar FIFA Jerome Valcke, ya aike da takarda ga shugaban hukumar NFF a Najeriya Aminu Maigari, don bayyana kudurin dage takunkumin da aka kakabawa Najeriyar.
A cewar Ademola, an soke takunkumin ne bayan da hukumar ta FIFA ta gamsu da cikar wasu sharuddan da ta gindaya a ranar 9 ga wata game da takunkumin.
Kafin hakan dai wata kotun kasar ta zartas da hukuncin dakatar da jami'an hukumar ta NFF daga aikin su, lamarin da ya sanya hukumar FIFA mayar da martani da matakin datakar da Najeriyar daga shiga dukkanin wasu wasanni da take tsarawa, ganin yadda a cewarta bai kamata hukumomi su rika tsoma baki cikin ayyukan hukumar gudanar da kwallon kafa mai zaman kanta ba.
Ana dai ganin takunkumin da hukumar ta FIFA ta sanyawa NFF ta Najeriyar ne, ya tilasawa gwamnatin kasar bukatar kotu ta janye hukuncin da ta yanke game da hukumar, matakin da kuma a yanzu zai baiwa kasar damar ci gaba da halartar gasannin kasa da kasa da hukumar FIFAr ke tsarawa.
Yanzu haka dai Najeriyar na da damar ci gaba da gudanar da shirin tinkarar wasannin share fagen gasar cin kofin duniya ta 'yan mata 'yan kasa da shekaru 20, da za ta gudana a kasar Canada a watan Agusta mai zuwa, gami da wasan share fagen gasar cin kofin nahiyar Afirka na matasa 'yan kasa da shekaru 17, wanda zai gudana a Kongo Kinshasa a ranar 27 ga watan Yulin nan, sakamakon janye takunkumin da FIFA ta sanyawa Najeriyar.