Hukumar wasan kwallon kafar kasar ta Algeriya ta sanar da hakan ne a ranar Asabar ta kan shafinta na yanar gizo. Haka kuma, an ce Gourcuff zai horar da 'yan wasan kungiyar kasar Algeriya, gami da 'yan wasa na kungiyar 'team A', wadanda ke taka leda a kuloflikan cikin gidan kasar.
Gourcuff mai shekaru 59 a duniya, wanda ya kasance tsohon kocin kulob din Lorient na kasar Faransa, zai fara aiki ne a watan Agusta mai zuwa. Bisa kwangilarsa da Algeria ta shekaru 4, zai jagoranci kungiyar Algeria da ake ma lakabin 'Desert Foxes', wajen halartar gasannin cin kofin nahiyar Afirka da za su gudana a Morocco a shekara mai zuwa, gami da a Libya a shekarar 2017. Haka kuma zai jagoranci kungiyar wajen neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za ta gudana a kasar Rasha a shekarar 2018.