An gudanar da wannan wasa ne dai a ranar 21 ga watan Yulin shekarar 2008, inda bangarorin 2 suka yi kunnen doki maras ci, abin da ya sanya Saliyo ta kasa samun damar ci gaba zuwa gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Afirka ta Kudu.
Dangane da wannan batu, ma'aikatar wasanni, da hukumar gudanar da wasannin kwallon kafa ta kasar Saliyo, sun ce sun tabbatar da samun cikakkun shaidu, kan yadda wasu jami'ai suka aikata mabudi, na sayar da wancan wasa, lamarin da a cewar hukumomin ya sabawa dokoki, da akidar wasanni da ma kishin kasa.
Saboda haka, hukumomin suka yanke shawarar dakatar da jami'an daga aikin su, da suka hada da 'yan wasa 5 dake buga ma kungiyar kwallon kafar kasar wasa, da darakta mai kula da wasanni Alphan Koker, da alkalai 3, da wani mai kulob din wasan kwallon kafa, da wani koci mai horar da 'yan wasa, da mambobin hukumar wasan kwallon kafar kasar su 3, gami da wani dan Lebanon mai kula da kungiyar wasan kwallon kafa.
Yanzu haka dai an riga an kafa wani kwamitin musamman domin gudanar da bincike kan wannan batu, sai dai ba a bayyana wa'adin aikin kwamitin ba tukuna.