in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta ci gaba da rike kambin ta na lamba daya, a gasar kasa da kasa ta kwallon hannu ta mata
2014-07-02 15:35:03 cri

Kungiyar kasar Sin ta mata 'yan kwallon hannu ta Volley ball, ta doke abokiyar karawar ta ta janhuriyar Dominican da ci 3 da nema, a wasan karshe da suka buga a ranar Asabar. Nasarar da ta baiwa kungiyar damar lashe wannan gasa a karo na biyu a jere.

'Yar wasar kungiyar ta Sin Hui Ruoqi ce dai ta ciwa Sin maki 14, yayin da kuma Liu Xiaotong ta samarwa kungiyar maki 11, sai kuma Yang Junjing da ta samu maki 10.

Don gane da wannan nasara da kungiyar ta Sin ta samu, mai horas da ita Lang Ping ta ce 'yan wasan ta sun yi kokari matuka sama da wasan su na ranar Juma'a wanda suka buga da kasar Belgium, koda yake ta ce akwai bukatar su kara karfafa kare gida a nan gaba.

A daya bangaren kuwa, kocin kungiyar janhuriyar Dominican Marcos Kwiek, yabawa 'yan wasan sa ya yi, sakamakon wasa da suka buga yadda ya kamata. Marcos ya ce duk da rashin nasarar da suka fuskanta, 'yan wasan sa sun yi kwazo kwarai, koda yake a cewar sa kasar Sin ta ci gajiyar 'yan kura-kurai da suka yi yayin wasan na karshe.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China