Rahotanni dai sun nuna cewa akwai wasu kuloflika da ke kokarin sayen sa, ciki har da FC Barcelona ta kasar Sifaniya. Jaridar Daily Mirror ta kasar Birtaniya ta ba da labarin cewa, Barca na shirin samar wa Suarez da wata kwangila ta tsahon shekaru 5, sai dai cikin kwangilar za a sanya wasu ayoyi na musamman don kayyade yadda zai gudanar da kwallo a kulaf din.
Jaridar ta labarta cewa, tun kafin Suarez ya fuskanci halin da yake ciki yanzu, FC Barca ta riga ta bayyana shi a matsayin dan wasa lamba 1 da take son dakkowa. Don haka, duk da cewa an hana shi buga wasu wasanni a nan gaba sakamakon wannan batu na cizo, ba a soke shirin da ake yi na zawarcin Suarez ba.
Haka nan an ce babban jami'in FC Barca mai kula da sashen nemo 'yan wasa, Andoni Zubizarreta, ya riga ya tattauna wannan batu tare da Lionel Messi, wanda shi ma ya nuna goyon baya sosai ga shigo da Suarez. Ban da haka kuma ya shawarce Barca da ta sayi dan wasan Argentina Sergio Aguero daga hannun Mancester City.
An ce kulob din Liverpool ya sanya wa Suarez farashin fam miliyan 80, farashin da FC Barca ta ce za ta yi shawarwari a kai tare da Liverpool. A hannu guda kuma Barca ta sanya wasu sharudda cikin kwangilar da za ta kulla da Suarez, ciki hadda cewa idan Suarez ya sake aikata abubuwan da basu dace ba za a ci tarar sa. Ban da haka kuma, Barca ta bukaci Suarez da ya nemi gafara daga wajen mutumin da ya cija.