in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Uganda ta sanar da 'yan wasan ta da za su buga gasar cin kofin kwallon kafa na 'yan kasa da shekaru 17
2014-06-12 19:03:02 cri
Daraktan tsare-tsare na hukumar kwallon kafar kasar Uganda Asuman Lubowa, ya bayyana jerin 'yan wasan kwallon kafar kasar da zasu buga gasar cin kofin kwallon kafar matasa 'yan kasa da shekaru 17 na nahiyar Afirka, yayin wasan farko da kasar za ta buga da kasar Seychelles.

Lubowa ya ce a yanzu haka sun yi shirin kai 'yan wasan na su birnin Jinja, domin su saba da yanayi, wanda ya yi kusa da na kasar Seychelles gabanin wasan na su da kasar Seychelles din a ranar 14 ga watan Yunin nan.

Har ila yau jami'in hukumar ya bayyana sunan Matia Lule a matsayin babban kocin kungiyar matasan.

Bisa tsarin wannan gasa dai kungiyar da ta samu nasara tsakanin Uganda da Sychelles ce za ta kara da kasar Rwanda a zagayen gasar na gaba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China