Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar, FENAPAF ta ce za ta mika wannan koke na ta gaban kotu a ranar Litinin mai zuwa. Kaza lika sanarwar mai dauke da sa hannun jagoran FENAPAF Rinaldo Martorelli, ta ce za ta bukaci a sauya lokutan wasannin da za a fara su tsakanin karfe 1 zuwa karfe 3 na yamma bisa agogon kasar, a yankunan Arewaci, da Arewa maso Gabashi, da kuma tsakiyar yammacin kasar, lokutan da a cewar kungiyar, ba za su dace da kariyar da ya kamata a baiwa lafiyar 'yan wasan ba.
Game da batun sanya lokacin sararawa ga 'yan wasa a cikin lokacin wasannin kuwa, sanarwar ta ce hakan na da nasaba da gwajin da aka yi a biranen Brasilia, da Manaus, da Frotaleza, da Sao Paulo, a watannin Yuni da Yulin bara, gwajin da ya nuna cewa awon zafin jikin 'yan wasa na iya haura digiri salsos 40, wanda hakan ke da hadari ga lafiyar su.
Kawo yanzu dai FIFA ba ta ce komai game da wannan batu ba tukuna.
Za dai a buga daukacin wasannin gasar cin kofin na duniya ne daga ranar 12 ga watan Yuni, ya zuwa 13 ga watan Yulin dake tafe.
Bisa kuma awon matsakancin yanayin zafin biranen kasar, birnin Manaus ne ke kan gaba a fannin zafi da digiri salsos 31, sai Cuiaba mai digiri salsos 30.7, sai Fortaleza mai digiri salsos 29.3, da Natal mai digiri salsos 29, yayin da kuma birnin Recife ke da digiri salsos 28.8. (Saminu Alhassan)