in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Akwai matsalar tsaro a Brazil inji mahukuntan kasar
2014-05-20 15:02:43 cri
Mahukuntan Brazil sun bayyana damuwa game da matsalar tsaro dake addabar kasar, kasa da wata guda a fara buga wasannin cin kofin duniya a kasar.

Da yake tsokaci game da wannan batu, ministan wasannin kasar Aldo Rebelo, ya shaidawa manema labaru a ranar Alhamis cewa, gwamnatin kasar na daukar dukkanin matakan da suka wajaba, don ganin an kare lafiyar 'yan kallon da za su halarci gasar ta cin kofin duniya dake tafe.

Yace batun tsaro matsala ce da ta dade tana damun kasar Brazil, sai dai daukacin sassan masu ruwa da tsaki na bada gudummawar da ta dace, domin shawo kan lamarin. A 'yan watannin baya dai mahukuntan kasar ta Brazil, sun sanar da ware dalar Amurka milyan 790, domin bunkasa aikin samar da tsaro a kasar.

Sai dai a yayin da masu ruwa da tsaki ke bayyana kudurin gwamnatin na daukar matakan duk da suka wajaba, domin magance matsalar ta tsaro, a hannu guda zanga-zangar kin-jinin gwamnati na ci gaba da wakana a kasar, inda ko da a a ranar Alhamis ma, sai da aka samu barkewar tarzoma a birnin Sao Paulo. Masu zanga-zangar dai sun yi alkawarin ci gaba da jerin gwano yayin gudanar da gasar cin kofin na duniya, bisa zargin da suke yi na kashe kudade masu yawa a shirye-shiryen gudanar da gasar, alhali kuwa muhimman ababen more rayuwar jama'a, kamar Asibitoci, da makarantu na fuskantar koma baya.

Game da wannan batu ministan wasannin kasar ya ce bai kamata masu kallon gasar kwallon kafa su damu ba, koda yake ya ce ba za a amince da duk wani mataki na tada zaune-tsaye ba. Kasancewar a cewar sa gwamnati ta dauki dukkanin matakan da suka dace bisa doron doka, ciki hadda kyale gudanar zanga-zangar lumana.

Game da batun filayen wasa kuwa, Mr. Rebelo ya ce dukkanin filayen wasan kasar 12 za su kammala kafin fara gasar. Duk kuwa da cewa 3 daga filayen, kawo yanzu ba a bude su ba a hukumce, wanda kuma bisa tsari hukumar FIFA ta tsaida watan Disambar bara a matsayin wa'adi na karshe na kammala aikin su.

Mr. Rebelo dai ya dage cewa kamar yadda aka samu nasarar gwajin nagartar filin wasan Curitiba, haka ma za a taras a Sao Paulo. Kuma dukkanin filayen wasan za su zamo cikin kyakkyawan yanayi lokacin gudanar gasar ta bana. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China